IQNA

UN Ta Yi Suka Kan Halin Da Fursunonin Siyasa Suke Ciki A Bahrain

22:03 - March 11, 2019
Lambar Labari: 3483448
Kwamitin katre hakkin bil adama na majalisar diniin duniya ya yi kakkausar suka dangane da halin da fursunonin siyasa suke ciki a kasar Bahrain.

kamfanin dillancin labaran iqna, Shafin yada labarai na Lu’ulu’a ya bayar da rahoton cewa,, a cikin rahoton da kwamitin kare hakkin bil adama na majalisar dinkin duniya ya fitar kan halin da fursunonin siyasa suke cikia  kasar Bahrain, ya yi kakkausar suka dangane da mawuyacin halin da suke ciki.

Bayanin ya ci gaba da cewa, bisa ga rahoton da kwamitin kare hakkin bil adama na majalisar duniya ya tattara kan halin da fursunonin siyasa suke ciki a kasar Bahrain, akwai wadanda suke rayuwa a wasu gidajen kurku da ba a kula das u.

Daga cikin matsalolin da suke fuksnata kuwa hard a yawan dauke musu wutar lantarki, da rashin isashen ruwa, ga kuma yaduwar cututtuka, kamar yadda kuma ake hana su gudanar da lamurransu bisa mahangarsu ta addini ko akida.

Tun daga ranar 25 ga watan Fabrarirun day a gabata ne kwamitin ya fara duba wannan batu, kuma za a ci gaba da bin bahasin har zuwa ranar 22 ga wannan wata Maris 2019.

3796875

 

 

 

captcha