IQNA

An kame Mutumin Da Ya Yi Barazanar Kashe ‘Yar Majalisar Dokokin Amurka Musulma

22:18 - April 07, 2019
Lambar Labari: 3483528
Jami’an tsaron kasar Amurka sun kame wani mutum dan shekaru 55 da haihuwa tare da gurfanar da shi a gaban kuliya, bayan da ya yi barazanar kisan ‘yar majalisar dokokin kasar musulma.

Kamfanin dillancin labaran iqna, kamfanin dillancin labaran reuters ya bayar da rahoton cewa, jami’an ‘yan sanda na birnin New Yorka  kasar Amurka sun sanar da cewa, mutumin da ya yi barazanar kashe Ilhan Omar ‘yar majalisar dokokin kasar Amurka ya shiga  hannu, kuma sun mika shi ga kotu.

Kotun birnin New York ta ce mutumin mai suna Patrick Carlinio ana zarginsa ne da yin barazanar kisan kai, wanda kuma idan aka tabbatar da laifin da ake zarginsa, to zai iya yin shekaru 10 a gidan kaso, tare da biyan tarar kudi da za su kai dala dubu 250.

Bayanin kotun ya ce bisa ga bayanan da ake da su, mutumin ya buga wayar tarho a ranar 21 ga watan Maris da ya gabata zuwa ofishin Ilhan Omar, inda ya yi magana da daya daga cikin ma’aikatan ofishin, inda ya sheda masa cewa yana da niyyar kashe Ilhan Omar har lahira.

A lokacin da ‘yan sanda ke masa tambayoyi, Patrick ya bayyana cewa, shi yana kishin kasarsa ne, kuma yana kaunar Donald Trump matuka, kuma yana tsananin kiyayya da ganin musulmi a  cikin gwamnatin Amurka.

Ilhan Omar dai ‘yar asalin kasar Somalia ce, wadda ta zama ‘yar majalisar dokokin Amurka karkashin inuwar jam’iyyar Democrat daga jahar Minnesota.

3801400

 

captcha