Tashar talabijin ta Russia Today ta bayar da rahoton cewa, kakain rundunar sojin gwamnatin Libya mai mazaunia Tripoli Muhammad Qanunu ya fadi jiya Talat a gaban manema labarai a birnin Tripoli cewa; sun kwace filin sauka da tashin jiragen sama na birnin, kuma yanzu yana karkashin ikonsu.
Ya ce a halin yanzu babu wata matsala a cikin birnin Tripoli, domin komai yana tafiya yadda ya kamata bisa doka da oda, kuma suna ci gaba da kara fadada yankunan da suke hankoron shimfida ikonsu a yankunan da ke gefen birnin Tripoli.
Muhammad Qanunu ya kara da cewa, suna da cikakken shirin tunkarar dakarun Haftar, kuma za su fatattake su daga dukkanin wuraren da suka yada zangoa kusa da birnin Tripoli.