IQNA

Limamin Juma’a: Matakin Da Majalisar Tsaron Kasa Ta Dauka Shi Ne Mafita

23:36 - May 10, 2019
Lambar Labari: 3483625
Hojjatol Islam Haji Ali Akbari, wanda ya jagoranci sallar juma’a  a birnin Tehran ya bayana cewa matakin da majalisar tsaron kasa ta dauka kan dakatar da aiki da wani bangaren yarjejeniyar nukiliya ya yi daidai da maslahar kasa.

Kamfanin dillancin labaran iqna, Limamin da ya jagoranci sallar Juma'a a birnin Tehran fadar mulkin Jamhuriyar Musulunci ta Iran ya jaddada cewa: Kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniya da kungiyar tarayyar Turai gami da sauran kasashe sun shiga wata babbar jarabawa.

A hudubar sallar Juma'arsa a yau a babban Masallacin birnin Tehran fadar Jamhuriyar Musulunci ta Iran, ya jaddada cewa: Samun hadin kai a tsakanin al'ummar Iran shi ne zai kai ta ga rusa duk wani makircin makiya.

Hujjatul-Islam Muhammad Jawad ya kara da cewa: Fushin da kasashen Turai suka yi kan matakin da Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta dauka na dakatar da yin aiki da wasu yarjeniyoyin da aka cimma da ita kan shirinta na makamashin nukiliya lamari ne da ke fayyace cewa: Kasar Iran tana kan ingantacciyar hanya da zata kai ta ga kare kyawawan manufofinta gami da hakkokinta da dokokin kasa da kasa suka tabbatar mata.

Hujjatul-Islam Jawad ya kuma jaddada cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta gindaya kwanaki sattin domin ganin kasashen yammacin Turai sun mutunta yarjejeniyar nukiliyar amma bayan cikan wadannan kwanaki, lallai Iran zata sake dauka wasu matakai domin mai da martani kan bakar siyasar da take fuskanta.

 

3810314

 

 

 

 

captcha