Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, a daren jiya sojojin yahudawa sun kai farmaki kan wasu matasa da suka taru a unguwar Alisawiyya da ke gabashin Quds domin nuna rashin amincewarsu da makircin da wasu kasashen larabawa suke kitsawa al’ummar Palestine.
Sojojin yahudawan sun bude wuta a kan matasan, inda harsashin bindiga ya samu Muhammad Samir Ubaid, wani matashi dan shekaru 20 da haihuwa, wanda bai jima da fitowa daga gidan kason yahudawan ba, a nan take ya yi shahada, wasu kuma suka samu raunuka.
Tun bayan faruwar lamarina daren jiya, sojojin yahudawan sun kafa shigaye da kuma hana shiga da fita a unguwar.