IQNA

Gwagwarmayar Falastinawa Ci Gaba Yunkurin Juyin Muslucni Na Iran Ne

23:56 - July 01, 2019
Lambar Labari: 3483797
Bangaren kasa da kasa, jakadan Palestine a kasar Iran Salah Al-zawawi ya bayyana cewa, gwagwarmayar falastina na a matsayin ci gaban yunkurin juyin juya hali na Iran ne.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a lokacin gudanar da wani taro kan ayyukan laifukan karni da Amurka ta aikata, wadaka gudanar a babban dakin taruka na farabia  jami’ar Amur Kabir, jakadan Palestine a Iran Salah Al-zawawi ya bayyana cewa, gwagwarmayar falastina na a matsayin ci gaban yunkurin juyin juya hali na Iran ne da tasirinsa.

Ya ci gaba da cewa marigayi Imam Khomeini (RA) da kuma jagoran juyin juya hali na yanzu Ayatollah Sayyid Ali Khamenei su ne jagororin al’ummar Falastine.

Dangane da muhimamncin hadin kai tsakanin dukkanin al’ummomin musulmi kuwa, ya bayyana cewa, dole ne dukaknin musulmi su hada kai domin tunkarar barazanar yahudawa a kan kasashensu da kuma wurarensu masu tsarki.

Haka nan kuma alokacin da ya koma kan batun cin zarafin al’ummomin larabawa da kuma muslmi da haramtacciyar kasar Isra’ila take yia  cikin falastine, ya bayyana cewa gwagwarmaya domin samun ‘yanci da daukaka ita kadai ce mafita ga al’ummar falastine.

Kamar yadda kuma ya bayyana abin da sarakunan larabawa suke da cewa abinkunya ne da kuma cin amana ga al’ummominsu, inda suke hada kai da yahudawa domin cutar da al’ummar Palestine.

3823640

 

 

captcha