IQNA

Dokar Ladabtar Da Masu Karkatar Da Tafsirin Kur’ani A Malaysia

23:43 - August 08, 2019
Lambar Labari: 3483926
Majalisar dokokin jahar Sabah a kasar Malaysia ta sanar da cewa za a kara tsauarar doka a kan masu juya tafsirin kur’ani yadda suka ga dama.

Kamfanin dillancin labaran ya habarta cwa, Idi Mukhtar babban kwamishinan shari’a a jihar Sabah a kasar Malaysia ya bayyana cewa, dokar mai lamba 52  a kudin tsarin dokoki na shekara ra 1995, ta tanadi wasu hukunce-hukunce ga wadanda suka sabawa doka kan sha’anin kur’ani.

Ya ce daga ciki akwai matakai na ladabtarwa  akan duk wanda ya yi amfani da son ransa wajen fassara ayoyin kur’ani, tare da karkatar da ma’anar zuwa ga manufarsa, ba a bin da ake nufia  cikin kur’ani ba

Daga ciki aki bulala da kuma biyan tara da ring 3000, ko kuma dauria  gidan kaso na tsawon shekaru biyu a kan duk wanda aka samu da aikata irin wannan laifi a jihar.

Babbar manufar kara tsarara wanann doka shi ne masu yin amfani da kur’ani da ayoyinsa wajen yaudarar matasa domin saka su cikin ayyukan ta’adanci da sunan addini.

3833110

 

 

captcha