IQNA

Nasrullah: Yakin Kwanaki 33 Shirin Amurka Ne

23:39 - August 17, 2019
Lambar Labari: 3483956
Bangaren kasa da kasa, babban sakataren kungiyar Hizbulallah ya bayyana yakin 33 a kan Lebanon da cewa shiri ne na Amurka.

Kamfanin dillancin labaran iqna, babban sakataren  kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon Sayyeed Hassan Nasrullah ya yi jawabi a kan allunan talabijin a garin Bintij-bel na kudancin kasar Lebanon a jiya jumma’a domin zagayowan ranar nasarar da kungiyar ta sami nasara kan sojojin Haramtacciyar kasar Isra'ila a yakin kwanaki 33 a shekara ta 2006.

A cikin jawabinsa a jiya jumma’a Sayyeed Nasrullah ya bayyana cewa manufar fara yakin shi ne shafe kungiyar Hinzbullah kwata-kwata a kasar Lebanon da kuma kawo karshen duk wani yunkuri wanda zai yi barazana ga samuwar haramtacciyar kasar.

Amma bayan yaki na tawon kwani 33 Isra'ila da kawayenta Amurka da sauransu sun tabbatar da cewa ba za su sami nasara a yakin ba, sai suka zabi tsagaita bude wuta da kuma kawo karshen yakin.

Sayyeed Nasaralla ya bayyana cewa nasarar da kungiyar hizbullah ta samu a shekara ta 2006 kan yahudawan, nasara ce ta dukkan mutanen kasar Lebanon da kuma sauran kungiyoyin masu gwagwarmaya a Palasdinu da sauran wurare a yankin.

Yakin watan yuli shi ne yakin da Isra’ila ta sha kashia  hannun dakarun Hizbullah wanda kuma shi ne shan kashi nafarko da mafi muni da ta yi a tarihi.

 

3835282

 

 

 

 

 

captcha