IQNA

Masallacin Birmingham Ya Lashe Kyautar Masallatai A Ingila

22:59 - September 11, 2019
Lambar Labari: 3484041
Bangaren kasa da kasa,a n zabi msallacin Birmingham a matsayin masallacin da yafi kowane masallaci a  Ingila a shekarar bara.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, Kamran Hussain daraktan masallacin Greenline da ke Birminghma ya bayyana cewa, su ne suka lashe kayutar masallatai ta shekarar 2018.

Ya ce wannan masallaci da aka gina shi kusan shekaru hamsin da suka gabata, ya jima yana gudanar da harkokinsa na addini, amma a shekarar bana aka fara gudanar da wanann gasa.

Wanann gasa dai an bayar da ita ne bisa la’akari da ayyukan da masallaci yake gudanarwa, kama daga fadakarwa da kuma da kuma kusanto da wadanda ba musulmi ba tare da kyautata musu da kuma nuna musu hakikanin kyakyawar koyarwa ta addinin muslucni.

A cikin shekara ta 1970 ne aka gina wannan masallaci, kuma masu gudanar da harkokin masallacin suna jawo mutane tare da basu kyautuka da kuma gayyatarsu buda baki a  lokacin azumi, da kuma lokutan taruka na musamman.

3841455

 

 

 

 

 

 

captcha