IQNA

Haramtacciyar Kasar Isra'ila Ta Kadu Dangane Da Bayanan Ayatollah Khamenei

12:43 - October 03, 2011
Lambar Labari: 2198020
Bangaren kasa da kasa, pira ministan haramtacciyar kasar Isra'ila ya bayyana matukar damuwarsa dangane da bayanan da jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran ya gabar a taron goyon bayan boren palastinawa karo na biya da aka gabatar.

Kamfanin dilalncin labaran iqna ya nakalto daga shfain sadarwa na yanar gizo na al-resalah cewa, Benyamin Natanyaho pira ministan haramtacciyar kasar Isra'ila ya bayyana matukar damuwarsa dangane da bayanan da jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran ya gabar a taron goyon bayan boren palastinawa karo na biyar da aka gabatar a nan birnin Tehran tare da halartar masana.
A lokacin da yake yin tsokaci dangane da manyan dalilan da suka haifar da samuwar kungiyoyin gwargwarmaya da ke dauke da makamai a Palasdinu a daidai lokacin da wasu ke yin kira da a gudanar da tattaunawa, jagoran ya ce yin amfani da hanyoyi na yaudara cikinsu kuwa har da kulla yarjejeniyar munafunci ta Camp David abubuwa ne da suka taimaka matuka domin samar da irin wadannan kungiyoyi a Palasdinu. Ayatullahi Sayyed Ali Khemenei ya ce abubuwan da suka faru kafin da kuma bayan kulla wannan yarjejeniya ta Camp David sun wajabta wa Palasdinawa ma'abota 'yanci daukar makamai dan kwato kasarsu daga hannun 'yan mamaya.

Jagoran ya ce akwai alamun samun nasara da kuma kawo karshen wannan mamaya ta Yahudawan Sahyuniyya, kuma hakan na kara tabbata idan aka yi la'akari da galabar da 'yan gwagwarmayar na kasar Labanan suka samu a kan yahudawa Sahyuniyya a shekara ta 2006, da kuma yadda al'ummar Gaza suka tsaya domin kare kasarsu a lokacin da yahudawan suka kaddamar da yaki a kansu a shekara ta dubu biyu da tara.

Ayatullah Ali Khemenei ya ce kwato illahirin kasar Palasdinu, ita ce babbar manufar wannnan gwagwarmaya amma ba samar da wani bangare na kasar da ke a hannun 'yan mamaya ba, inda ya ce a yau duniya ta shaidi cewa Amurka da kuma Yahudawan Sahyuniyya ba su da niyyar mutunta yarjeniyoyin da suka sanya wa hannu a tsakaninsu da Palasdinu, a maimakon hakan suna yayata cewa samar da kasashen biyu masu 'yanci wato Palasdinu da kuma Isra'ila ce hanya mafi dacewa domin wanzar da zaman lafiya a tsakanin al'ummomin biyu.

Jagaran na juyin musulunci ya ce tun daga shekarar 1948 lokacin da aka kirkiro da HKI ne Palasdinawa ke fama da matsaloli da suka hada da tilasta wa milyoyi daga cikinsu yin hijira zuwa wasu kasashe na waje tare kuma da hana wa 'yan gudun hijira dawowa zuwa kasarsu ta asali. A daya bangare na jawabinsa, Jagoran na juyin musulunci ya tunatar da duniya dangane da shawarar da Jamhuriyar musuluunci ta Iran ta bayar domin kawo karshen wannan rikici. 871353
captcha