IQNA

Wasikar Jagora Ta Bayyana Hakikanin Abin Da Ake Nufi Da Ta’addanci

23:38 - December 05, 2015
Lambar Labari: 3460122
Bangaren kasa da kasa, Danis Rankort ya bayyana sakon jagoran juyi a matsayin bayani kan hakikanin abin da ake nufi da ta’addanci a matsayi na duniya.


Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin facebook na Danis Rankort masani dan kasar Canada yana cewa sakon jagora na tarihin 29 ga watan Nuwanba, yana dauke bayani dalla-dalla kan ta’addanci da kuma yadda ya kamata a auna shi tare da gano hanyar magfance shi.

Ko shakka babu ayyukan ta’addanci da ake tafakwa a duniyar Musulunci wanda masu yinsa su ke daga tutar Musulunci yana da tashi rawar da ya ke takawa wajen bai wa masu kin addinin abinda za su fake da shi.

Wannan ne ya sa jagoran juyin musulunci Ayatollah Khamenei ya kira yi samari da matasan na turai da kada su kalli ‘yan ta’adda a mastayin masu wakilitar addinin Musulunci, maimakon hakan su koma ga alkur’ani mai girma da kuma rayuwar ma’aikin Allah da tarihinsa domin su fahimci hakikanin sakon addinin Musulunci.

Daya daga cikin abinda ya bai wa sakon na jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran, muhimmanci shi ne ba wai yana kiran samarin zuwa ga fahimtarsa dangane da addinin Musulunci ba ne kamar yadda ya ke cewa: “Ba ni yin naciya akan cewa fahimtata da Musulunci ko kuma wata fahimta ta daban ce kadai za ku karba, abinda na ke cewa shi ne kada ku  bari wannan yanayin da ya zama ruwan dare a duniyar wannan lokacin wanda ya ke kunshe da gurbatacciyar manufa ya zama ya yi lamba.

Bugu da kari, sakon na jagoran bai yi bayani akan shi kanshi musuluncin ba ta fuskar hakikaninsa, abinda ya maida hanakli akansa shi ne cewa hakki ne na dabi’a ga kowane mutum ya sami sani sanann kuma ya gudanar da bincike da nazari domin kai wa ga hakikar da ya ke nema.

Domin kuwa nesam sanin gaskiya wata dabi’a ce wacce ta ke tattare da kowane mutum.

Kiran da jagoran ya ke yi ga matasa da samarin nahiyar turai yana nufin cewa; Duk wata zuciya mai neman gaskiya ta hanyar komawa zuwa ga alkur’ani mai girma da kuma rayuwar manzon Allah za ta fahimci hakikanin koyarwar addinin Musulunci wacce ta ke cike da sa’adar rayuwa.

Ayatollah Khamenei a cikin karshen tawatan da ya gabata ne dai ya rubuta wata wasika zuwa ga matasan nahiyar turai wadda ta kunshi bayani kana bin da ake kira ta’addanci da ya kamata su fahimci banbancinsa da addin muslunci.

3459828

Abubuwan Da Ya Shafa: Rahbar
captcha