IQNA

An Bude Taron Shugabannin Majalisun Dokoki Na Kasashen Musulmi A Bagdad

22:13 - January 25, 2016
Lambar Labari: 3480077
Bangaren kasa da kasa, an bude babban taron shugabannin majalisun dokokin kasashen musulmi tare da halartar jamhuriyar muslunci ta Iran a birnin Bagadaza fadar mulkin kasar Iraki.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Bawwabah News cewa, an bude taron ne a yankin khadra na birnin Bagadaza.

Shugaban kasar ta Iraki Fua’d Ma’asum da kuma Firayi minista Haidar Abadi suna da wasu daga cikin manyan malaman addini gami da jami’a suna daga cikin wadanda suka halarci taron budewar.

Shugaban majalisar dokokin kasar Iran Ali larijani na daga cikin wadanda suke halartar taron, wanda kuma a yau zai gabatar da jawabinsa.

Babbar manufar gudanar da wannan taro dai ita ce tattauna hanyoyin shiga kafar wando daya da tsatsauran ra’ayi da ke kai musulmi shiga ayyukan ta’addanci da sunan addini a duniya.

Saga cikin kasashen da suke halartar taron akwai Pakistan, Turkiya, Algeria, Mali, Sudan, Kuwait, Syria, Tunisia, Somalia da sauransu, suna halartar taron na birnin Bagdad.

3469964

captcha