IQNA

Taron Tattaunawa Kan lamurran Addini Da Al’adu Tsakanin Iran Da Ghana

23:52 - March 27, 2016
Lambar Labari: 3480267
Bangaren kasa da kasa, an gudanar da zaman tattaunawa kan lamurra da suka shafi addini da kuma al’adu tsakanin Iran da kuma kasar Ghana.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na aynar gizo na bangaren sadarwa na cibiyar kula da harkokin al’adu a jamhuriyar uslunci ta Iran cewa, a jiya an gudanar da zaman tattaunawa kan lamurra da suka shafi addini da kuma al’adu tsakanin Iran da kuma kasar Ghana da kuma yadda za a kara bunkasa wannan bangare domin amfanin al’ummomin kasashen biyu.

A yayin bude taron George Batza shugaban kwalejin bincike kan harkokin addini a jami’ar Lagon Akra shi ne ya fara da gabatar da jawabinsa kan taron da kuma muhimmancinsa ga dukaknin bangarorin biyu.

Bayan nan kuma Rabiatu daya daga cikin malamn jami’ar ta gabatar da nata jawabin, inda ta bayyana cewa kasashen biyu suna abubuwa da dama da suka hada su, ta fuskar addini da kuma al’adu.

Haka nan kuma ta jaddada wajabcin kara bayar da himma daga bangaren cibiyar yada al’adun musluci a Iran wajen gudanar da harkoki na yada al’adu na muslunci da kuma tarihi a wadannan jami’oi da suke da dangantaka da su.

Shi ma a nasa bangaren karamin jakadan jamhuriyar muslunci ta Iran a kasar ta Ghana ya bayyana cewa, daya daga cikin abubuwa da suke da matukar muhimamnci a wannan lokaci a tsakanin al’ummomi shi ne kara fadada alaka ta aladu.

Domin kuwa acewarsa ta wannan hanya ma al’ummomi za su iya hada karfi da karfe domin fuskantar manyan kalu bale da suke ci wa duniya tuwo a kwarya a halin yanzu, musamman ma batun yaki da ta’addanci.

3484678

captcha