IQNA

Jagoran Juyi: 96 Shekarar Tattalin Arziki, Juriya, Samar da Ayyuka

Mutane Da Jagora Na Bukatar Shugabanni Sun Yi Kwazo Kan Ayyukan Cikin Gida

23:39 - March 20, 2017
Lambar Labari: 3481329
Bangaren siyasa, Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran, Ayatollah Ali Khamenei, ya isar da sakon taya murnarsa ga al'ummar Iran a kan shiga Sabuwar Shekara Iraniyawa ta 1396 Hijira shamsiya da aka shiga yau Litini.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin jagora cewa, jagoran juyin juya halin muslunci ya gabatar da jawabinsa na taya murnar sabuwar shekara ta shamsiyyah.

A Sakonsa na sabuwar shekara, Ayatollah Khamenei, ya soma da gabatar da murnarsa dangane da zagayowar ranar haihuwar 'yar Manzon tsira, Fatima Zahra (AS), tare da kuma fatan wannan sabuwar shekara ta zamantomai cike da tarin albarka da tsaro ga dukkan al'ummar Iraniyawa kama daga iyalan shahiddan kasar da wadanda suka samu raunuka a wajen yaki,dama duk sauran al'ummar musulmi.

Ayatollah Khamenei ya kira sabuwar shekara ta kalandar Iraniyawa da taken '' shekarar tattalin arziki dajuriya da kumasamar da ayyukan yi''

Jagoran ya kara da cewa ''duk da cewa matsalar tsaro na barazana ga kasar mu da kasashe makwafta da kuma yankin, ba mu taba yin wasa ba da al'amurran tsaro, kuma al'ummar kasarmu ta fahimci mine ne tabbatar da tsaro mai dorewa''

Sai dai a cikin jawabin nasaAyatollah Ali Khamenei, ya soki yadda gwamnatinkasar ke tafiyar da al'amuran tattalin arziki.

A sakon nasa ya ce yana da masaniya, kana kuma yana jin takaici dangane da halin da talakawa ke ciki, wanda ya danganta da kasawar gwamnatinkasar na biyan bukatun al'ummarta.

AyatollahAli Khamenei, ya kara da cewa akwai sakamako mai kyawo ta fuskartattalin arzikin gwamnati, amma akwai tazara mai yawa tsakanin abin da aka yi da abin da al'umma suka yi fatan gani daga gwamnati.

Jagoran ya zayyano matsalolin da suka hadarashin aikin yi, tsadar rayuwa,rashin daidaito da kuma matsalolin zamantakewa da ya ce mu dukkanmu muke fuskanta wadanda kuma a cewarsa dole mu dogara da Allah da al'ummarmu.

3585319

captcha