IQNA

Saudiyya Ce Ta Umarci Hariri Da Ya Yi Murabus

16:31 - November 06, 2017
Lambar Labari: 3482072
Bangaren kasa da kasa, jagoran kungiyar Hizbullah ya bayyana murabus din Saad Hariri da cewa shifta ce ta Saudiyya wadda bai isa ya tsallake ta ba.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, Shugaban kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon Sayyid Hasan Nasrallah ya bayyana cewar an tilasta wa firayi ministan kasar, Sa'ad Hariri, yin murabus ne daga Saudiyya ba bisa son ransa ba, yana mai kiran al'ummar kasar da su kai zuciya nesa da kuma ci gaba da kokari wajen tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankalin kasar.

Sayyid Nasrallah ya bayyana hakan ne cikin wani jawabi da ya yi dazu-dazun nan don karin bayani kan murabus din Sa'ad Haririn da kuma irin tuhumce-tuhumce marasa tushe da yayi wa kungiyar inda ya ce sanarwar murabus din Haririn ya zo ne bayan wasu ziyarce-ziyarce da ya kai kasar Saudiyya inda ya cematanin abin da Haririn ya karanto a matsayin sanarwar murabus s din nasa a fili yana nuni da cewa ba shi ya tsara shi ba face dai Saudiyya ce ta rubuta masa da tilasta masa karantawa.

Sayyid Nasrallah ya kara da cewa akwai yiyuwar murabus din Haririn na da alaka da rikicin neman mulki da ke faruwa a kasar Saudiyyan ko kuma watakila Saudiyyan ba ta jin dadin yadda yake gudanar da mulkinsa a Labanon din, kamar yadda ya ce akwai yiyuwar kuma Saudiyyan tana so ta dagula yanayin tsaro da zaman lafiyan kasar ta Labanon din ne, don haka sai ya kirayi al'ummar kasar musamman 'yan siyasa da su yi hakuri har hakikanin dalilin murabus din ya kara fitowa fili.

A jiya ne dai Sa'ad Haririn ya sanar da murabus din sa daga kasar Saudiyyan, cikin wani jawabi da yayi ta gidan talabijin din Al-Arabiyya na kasar Saudiyyan yana mai cewa yayi hakan ne saboda tsoron da yake da shi na cewa ana kokarin kashe shi, kamar yadda kuma ya zargi Iran da Hizbullah da tsoma baki cikin harkokin cikin gidan kasashen larabawa.

3660447


captcha