IQNA

Shugaba Rauhani Ya Isa Yankunan Da Girgizar Kasa Ta Shafa A Kermanshah

16:53 - November 14, 2017
Lambar Labari: 3482098
Bangaren siyasa, A yau da hantsi ne shugaba Rauhani na Iran ya isa yankin da girgizar kasa ta shafa a cikin Lardin kermanshah da ke yammacin kasar Iran, domin duba halin da al'ummar yankin suke ciki, musaman ma wadanda abin ya shafa.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, Bayan isarsa a yankin, shugabab Rauhani ya fara duba mutanen da suka samu raunuka, daga nan kuma ya duba wuraren da girgizar kasar ta yi barna.

Haka nan kuma shugaba Rauhani ya gana da jami'an da suke a wurin musamman na kiwon lafiya da kuma ma'aikatar cikin gidan, kan wajabcin ci gaba da kara bayar da himma wajen bayar da dukkanin taimakon da ya kamata ga al'ummar yankin.

Shugaba Rauhani ya bayyana cewa, gwamnatinsa za ta dauki alhakin bayar da dukkanin taimakon domin tabbatar da cewa an gyara dukkanin gidajen jama'a da suka rushe ko suka samu matsala sakamakon wannan girgizar kasa, haka nan kuma za a bayar da wani tallafin kudade na musamman ga dukkanin wadanda abin ya shafa.

Yanzu haka dai an mayar da wutar lantarki da iskar gas da kuma ruwan sha da suka yanke a wadannan yankuna. Yayin da kuma hukumomin bayar da agaji da na kiwon lafiya da jami'an soji suke ci gaba da taimaka ma mutane.

3663192


captcha