Wannan gasa dai tana daga cikin manyan tarukan da ake shiryawa akasar Bahrain domin gudanar da karatu da kuma hardar kur'ani a matsayi na kasa.
Abdulganiy Umar shi ne shugaban kwamitin shirya gasar kur'ani mai tsarki a kasar ya bayyana cewa, yanzu sun kammala dukkanin shirin da ya kamata domin daukar nauyin bakuncin wannan gasa.
Ya ce za a gudanar da taron bude gasar ne a masalalcin Alfateh da ke cikin birnin Manama, tare da halartar fitattun malamai da makaranta kur'ani daga kasar Masar, inda Ahmad Ahmad Nu'ainu shi ne zai bude taron da karatun kur'ani.
Daga cikin kasashen da za su halarta akwai Saudiyya, Oman, Masar, Aljeriya da kuma Chadi.
Ita dai wannan gasa an fara ta ne tuna cikin shekara ta 2014, kuma tana ci gaba a kowace shekara, wanda wanann shi ne karo na hudu.