Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na ina cewa, ana shirin gudanar da zaman taron ministocin harkokin al'adu an kasashen msuulmi a birnin kahrtum na kasar Sudan da nufin zabar birnin Sinnar a matsayin birnin al'adun muslunci na shekara ta 2017.
Bayanin ya ci gaba da cewa wannan tarin ana gudanar da shi ne a kowace shekara, akan zabi wani birni daga cikin biranan kasashen msuulmi da ke da tarihi ko kuma wata gudunmawa da ya bayar.
Kungiyar raya al'adun kasashen musulmi ta ISESCO ce take yin zaben, inda kwamitin kwararru na kungiyar kan yi zama domin fitar da birnin guda wanda ra'ayi ya zo daya a kansa.
Birnin Sinnar dai an zabe shi ne a matsayin birnin yawon bude ido na ababen tarihi.
Haka nan kuma taron wanda zai samu halartar ministocin harkokin wajen kasashen msuulmi, zai gudana ne har tsawon kwanaki uku a jere..
Abin tuni a nan dai shi ne, an zabi birnin Mashhad ne na kasar Iran domin karbar wannan matsayi, amma daga bisani kungiyar ta ISESCO ta sauya ra'ayinta saboda wasu dalilai da ba a sani ba.
Zama na farko dai ya gudana ne tuna a cikin shekara ta 1989 kuma ana ci gaba da gudanar da shi.