IQNA

Kahira Za Ta Dauki Nauyin Taron Yin Nazari Kan Rubutun Larabci

20:31 - November 15, 2017
Lambar Labari: 3482104
Bangaren kasa da kasa, ana shirin gudanar da taron kasa da kasa na yin nazari a kan rubutun larabci da kuma wasu ayyukan rubutu na muslunci.

Kamfanin dillancin labaran IQNA ya habarta cewa, cibiyar kula da ayyukan rubutun laraci ta duniya za ta shirya gudanar da taron kasa da kasa na yin nazari a kan rubutun larabci da kuma wasu ayyukan rubutu na muslunci tare da hadin giwa da jami’ar Switzerland.

Wannan taro dai za samu halartar masana daga kasashen duniya, da suka hada da musulmi da ma wadanda ba musulmi, domin yin nazari kan rubutun larabci.

Daga cikin cikin abubuwan da taron zai yi dubi a kans har da irin canje-canje da kuma ci gaban da rubutun larabaci ya samu a cikin tsawon tarihi, musamman ganin cewa kusan littafan addinin mulsunci da aka rubuta a tsawon tarihi duk a cikin harshen larabaci ne.

Baya ga haka kuma taron zai duba yadda ake yin amfani da hashen a wasu ilmuka na daban a halin yanzu duk da cewaa baya an yi amfani da shi wajen rubutun ilmomi daban-daban, wanda hatta masanan yammacin turai sun dauki wasu ilmomin daga musulmi, wada kuma an rubuta ne da harshn laraci, sai kuma harshen farisanci.

A yayin zaman taron zaman taron za a baje kolin wasu daga cikin dadaddun littafai da aka rubuta daruruwan shekaru da ska gabata, tare da kwatanta yanayin rubutun da littafai na wannan zamani da aka rubuta da naura.

Wannan cibiya dai ta fara aikinta e tun a cikin shekara ta 1946 a birnin Alkahira na kasar Masar.

3663785


captcha