IQNA

An Dora Tutar Juyayin Wafatin Ma'aiki (SAW) A Kan Hubbaren Alawi

12:57 - November 16, 2017
Lambar Labari: 3482105
Bangaren kasa da kasa, masu hidimar a hubbaren Amirul muminin (AS) da ke Najaf sun dora tutar juyayin wafatin manzon Allah a kan ginin hubbaren.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na bangaren hulda da jama'a a hubbaren Aalwi cewa, a jiya masu hidimar a hubbaren Imam Ali (AS) da ke Najaf sun dora tutar juyayin wafatin manzon Allah a kan tulluwar hubbaren mai tsarki.

Bayanin ya ci gaba da cewa bisa ga al'ada wannan taro nana gudanar da shi a kowace shekara, domin yin juyayi da alhini kan wafatin manzon rahma tsira da amincin Allah su tabbata gare shi da iyalan gidansa tsarkaka.

Baya ga dora tuta kan tulluwar hubbaren mai tsarki, ana gabatar da jawabai da suka shafi rayuwar ma'aiki da kuma kissoshi da suka shafi wafatinsa da wasicinsa.

Bisa ga ruwayoyi ad suka inganta daga ahlul bait (AS) manzon Allah (SAW) ya rasu ne a ranar 28 ga watan safar shekara ta 11 bayan hijira, kuma dan uwansa Imam Ali (AS) ne ya jagoranci janazarsa.

3663649


captcha