IQNA

Matakan Tsaro A Najaf A Lokacin Tarukan Wafatin Manzon Allah (SAW)

16:51 - November 16, 2017
Lambar Labari: 3482106
Bangaren kasa da kasa, gwamnan Najaf ya bayyana cewa sun dauki dukkanin matakan da suka dace domin gudanar da tarukan zagayowar lokacin wafatin manzon Allah (ASW) a birnin.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, Lui Alyasir gwamnan Najaf ya bayyana cewa sun dauki dukkanin matakan da suka dace domin gudanar da tarukan zagayowar lokacin wafatin manzon Allah (ASW) da za a yi gobe a birnin mai alfarma.

Ya ce yanzu haka dukkanin bangarorin tsaro da suka hada da sojoji, ‘yan sanda da jami’an tsaro na farin kaya gami da dakaru masu aikin sa kai na hashd Sha’abi, sun kammala dukkanin shirinsu tare da kafa shingayen tsaro a dukkanin titunan birnin da muhimamn wurare, gami da hanyoyin da ke isa birnin daga sauran larduna.

Gwamnan na Najaf ya ce, nauyi da ya rataya a kansu ad su gudanar da dkkanin sare-tsare domin bayar da kariya ga masu ziyara da kuma halartar tarukan wafatin manzon Allah a hubbaren Imam Ali (AS) da ke birnin.

A lokutan baya dai an samu ‘yan ta’addan wahabiyya mas kiyayya da da shi’ar ahlul bait (AS) da ske kai hare-haren bama-bamai a wadannan taruka, wadanda was kasashen larabawa suke daukar nauyinsu.

3664123


captcha