IQNA

Inganta Ayyukan Kwamitocin Masallatan Morocco A Holland

23:38 - November 17, 2017
Lambar Labari: 3482109
Bangaren kasa da kasa, shirin gudanar da wasu ayyuka na inganta ayyukan masallatan Morocoo a kasar Holland.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, shafin yada labarai na aabbir.com ya habarta cewa, an kafa wani kwamiti wanda kunshi mambobin masallatai 23 a kasar Holland, domin tattauna yadda za a sake sabon fasali na tafyar da ayyukansu.

Babbar manufar yin hakan dai ita ce sanya birki ga masu yin amfani da masalatai wajen yada akidar ta’addanci a cikin kasashen turai, musamman ma bayan bullar akidar nan ta takfiyya wadda ta samo tushe daga wahabiyanci.

Marzuk Aulad Abdullah babban limamin masallacin Juma’a na birnin Amstardam ya bayyana cewa, ko alama ba za su taba bari a mayar da masallatansu wajen yada akidar da ke saka matasa a cikin ta’addanci da sunan muslunci ba.

‘Yan kasar Moroco da suke zaune a kasar Holland suna da masallatai, wadanda ae kira da masalatan Morocco.

3664278


captcha