IQNA

Rahoto Kan Cin Zarafin Bil Adama A kasar Myanmar

23:39 - November 17, 2017
Lambar Labari: 3482110
Bangaren kasa da kasa, Kwamiti na uku a babban zauren MDD ya fitar da wani sabon kuduri wanda ya yi Allah wadai da gwamnatin kasar Myanmar kan yadda take azzabtar da musulman kasar Myanmar.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a jiya Alhamis ne komiti na ukku a babban zauren majalisar dinkin duniya ya sake yin kira ga gwamnatin kasar Myanmar ta dakatar da ayyukan sojojin kasar namusgunawa al-ummar musulmi Rokhinga, ta kuma amince da hakkokin mutanen kabilar Rokhinga a matsayin yan kasar ta Myanmar.

Wannan kudurin dai ya sake farfado da wasu irinsa a baya wadanda suka sanya aka dakatar da kasar ta Myanmar a matsayin kasa wacce take kare hakkin bil'adama.

A zaben yarda da wannan kudurin akomitin na ukku a jiya Alhamis, wakilan kasashen duniyadari da talatin da biyar ne suka amince da shawarorin da aka gabatara a cinkinsa a yayinda wasu kasashe goma suka ki amincewa. Sai kuma wasu wakilai 26 da suka kauracewa zaben.

A cikin wannan sabon kuduri dai an bukaci babban sakataren MDD Antonia Goterres ya nada jakada na musamman kan lamuran kasar Myanmar. Wannan komitin dai yakan samar da kuduri kan matsalolin take hakkin bil'adama a kasar Myanmar a ko wace shekara, har na shekaru sha biyar da suka gabata.

3664072


captcha