IQNA

Taron Karatun Kur'ati Tare Da Halarta Makaranta 20 A Iraki

19:49 - November 18, 2017
Lambar Labari: 3482111
Bangaren kasa da kasa, an gudanar da wani taron karaun kur'ani mai tsarki a lardin Ziqar na kasar Iraki tare da halartar fitattun makaranta kur'ani na kasar.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya ahbarta cewa, an gudanar da wani taron karaun kur'ani mai tsarki a lardin Ziqar na kasar Iraki tare da halartar fitattun makaranta kur'ani na kasar domin tunawa da zagayowar lokacin wafatin manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalan gidansa.

Wannan taro dai ya samu halartar wadannan fitattun makaranta ne daga dukkanin sassa na kasar, wadanda suke bayar da gudunmawa wajen yada lamarin kur'ani mai tsarkia tsakanin al'ummar Iraki.

Makaranta kur'ani dai suna da gagarumar rawar da suke takawa wajen jan hankulan al'umma domin komawa zuwa ga lamarin kur'ani, da ya hada da karatunsa da kuma koyan ilmominsa.

Matasa dai su ne suka fi amfanuwa da irin wannan shiri na kur'ani domin kuwa amafi yawan lokuta sue n suka halartar wuraren da ake gudanar da shirin.

Yanzu haka dai an kammala dukaknin tarukan tunawa da wafatin manzon Allah da aka gudanar a mafi yawan lardunan kasar Iraki a jiya.

3664380


captcha