IQNA

Bayani Kan Koyarwar Kur'ani Kyauta A Amurka

19:54 - November 18, 2017
Lambar Labari: 3482113
Bangaren kasa da kasa, wasu daga cikin musulmin birnin Las Cruces na Amurka sun kirkiro da wani shirin wayar da kan mutane kan muslunci.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Las Cruces cewa, wasu daga cikin musulmi suna kokarin ganin sun ci gaba da aiwatar da wani shiri da suka fara na wayar da kan mutane akan musulunci.

Surayya Hussain wata lauya ce musulma a wannan jaha ta New Mexico, ta bayyana cewa sun kirkiro da wannan shirin da nufin ganin sun bayar da dama ga wadanda ba musulmi da su iya sanin wani abu a kan addinin muslunci.

Tun kafin wannan lokacin dai wasu daga cikin cibiyoyon musulmi sukan gayyaci jama'a da su halarci wuraren tarukansu musamman ma masallatai, domin ganin yadda suke yin ibada, da kuma amsa tambayoyin da jama'a suke da su a kan addinin muslunci.

Wannan shiri dai ya zo ne sakamakon irin kyamar muslunci ke ci gaba da karuwa a kasar, musamman a cikin wadannan lokuta, bayan kafa sabuwar gwamnati da tazo da taken kin jinin muslunci da kyamar baki.

3664412


captcha