IQNA

China Na Daukar Matakan Yin Leken Asiri A Kan Musulmin Kasar

23:36 - January 19, 2018
Lambar Labari: 3482314
Bangaren kasa da kasa, gwamnatin kasar China na yin liken asiri a kan musulmin kasar ta hanyar yin amfani da naurorin daukar hoto.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na scmp cewa, a cikin kwanakin nan gwamnatin kasar China na yin liken asiri a kan musulmin kasar ta hanyar yin afani da naurorin daukar hoto musamman a garin Sin gyang.

A halin yanzu haka dai dukkanin manyan titunan birnin Sin Gyang cike suk da kamarorin daukar hotunan mutane a ko’ina, domin sanya ido a kan dukkanin harkokinsu da sunan yaki da ta’addanci.

Wannan matakin dai ba shi ne na farko ba, domin kuwa musulmin kasar China wadanda su ne marassa rinjaye a kasar sun jima suna fuskantar matsaloli da takura daga gwamnatin gurguzu ta China.

Haka nan kuma an saka dokoki masu tsauri a yankin tare hana musulmi nuna rashin amincewarsu da ko saba ma dokokin, wanda yin hakan yana tattare da babbar ukuba.

Daga cikin matakan tarukara da gwamnatin China take dauka  akan musulmi, har da hana saka sunayen musulunci ga yaran da ake haihuwa, da hana saka hijabi, da kuma hana gudanar da tarukan addin da hana koyar da karatun kur’ani, haka nan kuma ana tilasta ma musulmi kallon tashoshin talabijin na gwamnati.

3683226

 

 

 

captcha