IQNA

An Fara Shirin Zagayowar Ranar Hijabi Ta Duniya

22:46 - January 21, 2018
Lambar Labari: 3482321
Bangaren kasa da kasa, an fara gudanar da shirye-shirye domin ranar hijabi ta duniya kasa da makonni biyu masu zuwa.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin yada labarai na Times Headline cewa, an fara gudanar da kamfe mai take #StrongInHijab domin zagayowar ranar hijabi ta duniya.

Mata musulmia  koina cikin fadin duniya rubuta abin da suke bukata fada dangane da hijabi suna turawa shafukan zumunta.

A ranar hijabi ta duniya mata suna saka nauoin hijabi tare da gudanar da taruka na wayar da kai kan muhimmanci hijabi da kuma matsayinsa  a cikin addinin muslunci.

Haka nan kuma mata sukan bayar da kyautuka na musamman ga ‘yan uwansu mata wadada ba musulmi ba, tare da gayyatarsu zuwa gidajensu  ko kuma wasu wuraren taruka na musamman da ake shiryawa a ranar kan hijabi.

A kan bayar da hijabi ga masu bukata domin saka a wannan ranar, domin su ji yadda musulmi suke ji, domin su gane cewa hijabi tufafi ne ba wani abin tsoro bane, domin su daina yi musulmi mata masu yin lullubi wani kallo na daban.

Dukkanin  addinai da aka saukar daga sama dai sun yi umarni da saka hijabi, kamar yadda addinin musulunci da ya zo karfafa wannan lamari  kamar yadda yake a  sauran addinai da aka saukar daga sama.

An fara gudanar da ranar hijai ne cikin shekara ta 2013 a kasar Amurka, sakamkon cin zarain da mata musulmi masu saka lullubi suke fuskata daga wasu masu kyamar musulunci.

3684076

 

captcha