IQNA

Sayyid Hassan Nasrullah:

Takaita Hare-Hare Kan Syria Ya Nuna Makiya Sun Amince Da Karfin Gungun ‘Yan Gwagwarmaya

23:30 - April 15, 2018
Lambar Labari: 3482571
Bangaren kasa da kasa, jagoran kungiyar Hizbullah ya bayyana cewa, takaita hare-haren da Amurka ta jagoranta kan Syria ya tabbatar da karfin sojin Syria da gungun masu gwagwarmaya.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani jawabi da ya gabatar a yammacin yau,  jagoran kungiyar Hizbullah a Lebanon Sayyid Hassan Nasrullah ya bayyana cewa, takaita hare-haren da Amurka ta jagoranta kan Syria ya tabbatar da karfin sojin Syria da gungun masu gwagwarmaya da suke kawance da sojojin na Syria.

Ya ce Amurka ta fi kowa sanin cewa batun amfani da makami mai guba  a Syria wasan kwaikwayo ne, amma ta fake da hakan ne domin ta nuna wa ‘yan ta’adda da suka sha kayi a hannun dakarun Syria cewa tana tare da su.

Kuma Amurka ta san da cewa shiga yaki da sojin Syria da kuma masu kawance da su ahalin yanzu ba a bu ne mai sauki gare ta ba, domin bata san inda yakin zai kare ba, da kuma irin asarorin da za ta, domin ta san cewa zai sha banban da yake-yaken da ta yi a wasu kasashen, domin kuwa mafi yawan makaman da ta harba a kan Syria an kakkabo su.

 

3705876

 

captcha