Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, shafin yada labarai na Lu'ulu'a ya bayar da rahoton cewa, a cikin makon nan ana gudanar da gangami a kasashe daban-daban da suka hada da Turkiya, Switzerland, Pakistan Birtaniya domin yin kira ga gwanatin tarayyar Najeriya da a saki Sheikh Zakzaky da ake tsare da shi.
Wannan gangami da jamaa suke gudanarwa a kasashen duniya daban-daban sakamako na kiran da kungiyar kare hakkokin musulmi a kasar Ingila ta yi ga kungiyoyin musulmi daban-daban a nahiyar turai, kan su matsa lamba kan majalisar dinkin duniya domin ganin an sakin malamin
Tun a karshen watan Disamban shekara ta 2015 ne dai jami'an sojin Najeriya suka kaddamar da farmaki a kan gidan malamin a zaria da kuma cibiyar da suke gudanar da tarukan addini, inda sojojin suka kasha daruruwa daga cikin mabiyansa da suka hada har da 'ya'yansa uku.
Tun daga lokacin kuma ake ci gaba da tsare shi tare da mai dakinsa, kuma magoya bayansa na ci gaba da gangami domin neman a sake shi kamar yadda kotu ta bayar da umarni, amma gwamnatin Najeriya ba ta sake shi ba.