IQNA

MDD Ta Nuna Damuwa Matuka Dangane Da Hare-Haren Saudiyya Hodedah Yemen

23:55 - June 14, 2018
Lambar Labari: 3482757
Bangaren kasa da kasa, Majalisar Dinkin Duniya, ta ce tana ci gaba da tattaunawa domin kaucewa zubar da jini a birnin Hodeida na kasar Yemen, inda kawancen da Saudiyya ke jagoranta ya kaddamar da hari a yau Laraba.

 

Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, Kawancen da Saudiyyar ke jagoranta tare da hadaddiyar daular larabawa, na kai hare hare da suka hada dana sama da na ruwa a yankin Hodeida da nufin kwace shi daga hannun 'yan gwagwarmaya neman sauyi na Houtsis.

Wakilin musamman na MDD, a Yemen,  ya bayyana a wata sanarwa cewa yanzu haka suna tuntubar dukkan bangarorin da batun ya shafa, domin samar da wata mafita ta kaucewa dagule al'amura a yankin.

Sanarwar ta ce cikin hanyoyin da ake neman daidaito akansu don samun zaman lafiya sun hada da siyasa, agaji da kuma tsaro da suka shafi dukkan bangarorin.

Kaddamar da farmakin a birnin na Hodeida, wanda ya kunshi tashar ruwan Hodeida, kan iya jefe rayuwar fararen hula cikin tsaka mai yuwa, kasancewar nan ne ake shigar da yawancin kayan agajin da ake shigar dasu a kasar ta Yemen, dake fama da yaki.

MDD, dai ta yi kira da kakkausar murya da a dakatar da yaki a kasar ta Yemen, da kuma lalubo hanyoyin samar da zaman lafiya ta hanyar siyasa.

 

3722796

 

 

 

captcha