IQNA

Rasha Ta Yi Gargadi Dangane Da Hare-Haren Da Mayakan Hadi Mansur A Hodaidah

23:59 - June 14, 2018
Lambar Labari: 3482759
Bangaren kasa da kasa, ma’aikatar harkokin wajen kasar Rasha ta yi gargadi dangane da halin da za a jefa al’ummar Yemen sakamakon hare-haren mayakan Hadi a gabar ruwan Hodaidah ta Yemen.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, kamfanin dillancin labaran sputnik ya habarta cewa, a cikin bayanin ma’aikatar harkokin wajen kasar ta Rasha, ta bayyana cewa daukar matakin kaddamar da yaki kan Hdaidah ba maslaha ce ba.

Bayanin y ace wannan ita kadai ce sauran hanyar da ta rage ga al’aummar Yemen da suke samun agaji na abinci da magunguna, wanda rusa wannan tashar ruwa na nufin karasa sauran al’ummar Yemen da suka rage a raye a halin yanzu.

Mayakan Hadi Mansur da suke samun dauki daga Saudiyya da Amurka da Isra’ila, suna hankoron ganin sun kwace iko da gabar ruwan Hodaidah wadda al’umma Yemen suke samun abinci da taimakon magunguna ta wannan hanya.

3722833

 

 

captcha