IQNA

An Kawo Karshen Gasar Kur’ani Ta Iran A Uganda

23:42 - June 17, 2018
Lambar Labari: 3482766
Bangaren kasa da kasa, an kawo karshen gasar karatu da hardar kur’ani da Iran ta shirya a kasar Uganda.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na bangaren hulda da jama’a na cibiyar yada ala’adun musulunci cewa, an kawo karshen gasar karatu da hardar kur’ani da Iran ta shirya a kasar Uganda kamar yadda aka saba yi  a kowace shekara.

Ali Bakhtiyari shi ne shugaban ofishin kula da harkokin al’adu na kasar Iran a Uganda, shi ne ya jagoranci taron rufe gasar, tar da halartar wasu daga malaman addini na kasar da kuma wasu jami’an gwamnati.

Wanann gasa ta hada da bangaren harda da kuma karatun kur’ani, inda kasar ta Iran ta dauki nauyin gasar baki daya, wadda ta samu halartar daruruwan musulmi matasa.

Ita dai wanan gasa bisa al’ada an afara gudanar da ita ne a cikin watan azumin Ramadan, kuma a kammala ta bayan kammala azumin Ramadan.

An bayar da kyautuka ga dukkanin wadanda suka shiga gasar, kamar yadda kuma aka bayar da kyautuka na musamman ga wadanda suka nuna kwazo.

3723254

 

 

captcha