Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, martin Griffiths manzon musamman na majalisa dinin duniya kan rikicin Yeman, a yammacin yau zai halaci zaman kwamitin tsaron majalisar dinkin duniya wanda zai gudanar kan batun rikicin kasar Yemen a asirce.
Zaman zai duba batun shawarar da majalisar dinkin duniya ta gabatar wa kungiyar Ansarullah ne kan ta janye daga gabar ruwan Hudaida da kasashen da suke yaki da yemen suke son karbewa, shawarar da Ansarullah suka ki amincewa da ita, amma dai sun bukaci a basu lokac su yi tunani kan wasu batutuwan da aka gabatar musu.
Martin Griffiths manzon musamman na majalisa dinin duniya kan rikicin Yeman a yau ne yake barin birnin San’a domin halartar zaman taron na kwamitin tsaro.