IQNA

Taro Mai Taken Matsayin Shariffai A Musulunci A Senegal

23:57 - June 28, 2018
Lambar Labari: 3482794
Bangaren kasa da kasa, za a gudanar da wani taro mai taken matsayin sharifai a a cikin addinin muslunci a kasar Senegal.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, karamin ofishin jakadancin Iran tare da wasu cibiyoyin addini za su gudanar da wani taro mai taken matsayin sharifai a a cikin addinin muslunci a kasar Senegal a yankin Dangan, ami tazarar kilo mita 160 daga birnin Dakar.

Wannan taro da za a gudanar a ranar Asabar mai zuwa zai samu halartar manyan malaman dariku na sufaye gami da wasu jami'ai.

Sharifai dai suna da matsayi na musamman a cikin zukatan al'ummomin musulmi a nahiyar Afirka, inda akan basu girma da kima kasantuwar ana danganta su da jinin ma'aiki tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da alayensa tsarkaka.

3726023

 

 

 

 

 

 

captcha