IQNA

Hasashe Ya Nuna Cewa Adadin Musulmi A Duniya Zai Karu

22:52 - September 02, 2018
1
Lambar Labari: 3482946
Bangaren kasa da kasa, Wani hasashen da wata cibiyar bincike ta yi ya nuna cewa nan da shekara ta 2060 adadin musulmi a duniya zai haura biliyan uku.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, tashar radiyon RTL ta kasar Faransa ta bayar da rahoton cewa, a nazarin da wata babbar cibiyar bincike ta Pew Center da ke kasar Amurka ta yi, ta bayyana cewa bisa la'akari da karuwar musulmi a duniya, adadinsu zai kai biliyan 3 da doriya a cikin shekara ta 2060, idan aka yi la'akari da yawansu da ya kai biliyan 1.6 a cikin shekara ta 2010.

Cibiyar ta ce a halin yanzu mafi yawan musulmi suna zaune a yankunan tsakiyar Asia da kuma gabashinta da kuma kudanci, inda kashi 62 cikin dari na musulmin duniya suna a cikin wadannan yankunan ne.

Sauran musulmin kuma suna a cikin yankunan gabas ta tsakiya ne da arewacin Afirka, kamar yadda kuma sauran yankunan Afrika na bakaken bata za su zo a matsayi na uku, sai kuma sauran yankuna da suka hada da nahiyar turai, Amurka da kuma Latin, inda a dukkanin wadannan nahiyoyi adadin musulmi yana karuwa ne.

Sakamakon binciken cibiyar ya nuna cewa, baya ga hayayyafa da musulmi suke yi musamman kasashen ad suka fi yawa, a daya gefen kuma addinin muslucni shi ne addinin da ya fi saurin samun masu karbarsa fiye da dukkanin sauran addinai na duniya.

3743171

 

 

Wanda Aka Watsa: 1
Ana Cikin Dubawa: 0
Ba A Iya Watsa Shi: 0
Ba A San Shi Ba
0
0
Banyi mamakiba sabida Allah ta ala yafadama hakan yana nan zaifaru kuma munyi imani akan hakan
captcha