IQNA

Farmakin Sojin Isra’ila A Kauyen Kafarqudum

23:41 - October 15, 2018
Lambar Labari: 3483044
Bangaren kasa da kasa, Sojojin yahudawan Isra’ila sun kai farmaki a kan kauyen Kafarqudum da ke karkashin yankin Nablus a gabar yamma da kogin Jodan.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, Bisa rahoton da kamfanin dillancin labaran Ma’an News ya bayar, sojojin yahudawan sun kai farmakin ne da nufin lalata wani babban bututun da ke kai wa kauyen ruwan sha daga garin Nablus.

Mazauna kauyen sun yi dauki ba dadi da sojojin yahudawan, inda suka yi kokarin hana yahudawan isa zuwa yankin da bututun yake, amma sun yi amfani da karfi wajen tarwatsa mutane, kuma daga karshe sun lalata bututun, wanda ta hanyarsa ne al’ummar kauyen ke samun ruwan sha.

A cikin shekara ta 2003 ce dai gwamnatin yahudawan Isra’ila ta kafa wani matsugunnin yahudawa ‘yan share wuri zauna na Kedumim, wanda ya raba Nablus da kauyen na Kafarqudum.

3755801

captcha