IQNA

Ma'aikatar Harkokin Wajen Iran Ta Mayar Da Martani Kan Takunkumin Amurka

22:52 - November 03, 2018
1
Lambar Labari: 3483094
Bangaren siyasa, ma'aikatar harkokin wajen kasar Iran ta mayar da martani dangane da sabbin takunkuman da gwamnatin kasar Amurka ta kakba wa kasar ta Iran.

Kamfanin dilalncin labaran iqna, a cikin bayanin da ta fitar a yau Asabar, ma'aikatar harkokin wajen kasar Iran ta bayyana sabbin takunkuman na Amurka da cewa ba za su daga wa Iran hankali ba, domin kuwa kasar dama ta dogara da kanta ne, kuma za ta ci gaba da bin nata hanyoyin domin ci gaba da karfafa tattalin arzikin kasr.

Bayanin na maaikatar harkokin wajen kasar ta Iran ya ce; abin da Amurka ta yi ya kara tabbatar wa duniya da cewa, ita ba kasa ce da take girmama dokoki da ka'idoji na duniya ba, domin ficewa daga yarjejeniyar nukiliya ta duniya kan shirin Iran da Amurka ta yi ya sabawa kudirin majalisar dinkin duniya.

Dangane da batun hana Iran sayar da danyen mai kuwa, bayanin ya ce amurka ba ta isa ba, domin kuwa ba dukkanin kasashen duniya ne suka taru suka zama bayinta ba.

Haka nan kuma baynin ya ja hankalin gwamnatin Amurka da cewa, dukkanin abin da take yi maimaici ne na gwamnatocin Amurka da suka gabata, kuma bayan karewar wa'adin wannan gwamnati jami'anta za su dawo su yi nadama, domin kuwa ba za su taba cin nasara  akan bakaken manufofinsu ba.

Daga karshe bayanin ya jinjina wa kasashen kungiyar tarayyar turai da suka yi Allawadai da matakin na Trum a kan Iran, musamman ma kasashen da suka rattaba hannu kan yarjejeniyar, wato Birtaniya, Faransa da kuma Jamus, da kuma babbar jami'a mai kula da harkokin wajen siyasar tarayyar turai Federica Mogherini.

3760846

 

Wanda Aka Watsa: 1
Ana Cikin Dubawa: 0
Ba A Iya Watsa Shi: 0
Ba A San Shi Ba
0
0
SLM YA ALLAH YAKARE MUSULMI DA MUSULUCI A MEEN DAGA FARUKU SOKOTO YABO BULAGA
captcha