IQNA

Gyaran Kur'ani Mai Tarihin Shekaru 600 A Yemen

22:39 - November 08, 2018
Lambar Labari: 3483112
Bangaren kasa da kasa, za a gudanar da wani kin gyaran wani dadden kwafin kur'ani mai tsarki mai shekaru 600 a kasar Yemen.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga jaridar Thaura cewa, ana shirin gudanar da wani kin gyaran wani dadden kwafin kur'ani mai tsarki mai shekaru 600 birnin San'a fadar mulkin kasar Yemen.

Bayanin ya ce cibiyar Sha'ab mai kula da adana kayan tarihi ta kasar Yemen ita ce za ta gudanar da wannan aiki na gyaran kur'ani mai shekaru 600 da rubuta, wanda ake ajiye da shi a dakin ajiye kayan tarihi na kasar a birnin San'a.

Shugaban cibiyar ta Sha'ab ya bayyana cewa, za  agudanar da wannan aiki ne tare da hadin gwiwa da ma'aikatar kula da harkokin ala'adu ta kasar.

3762227

 

 

 

 

 

captcha