IQNA

Kotun Turkiya Ta Bayar Da Umarnin Kame Masu Hannu A Kisan Khashoggi

23:08 - December 05, 2018
1
Lambar Labari: 3483182
Babbar kotun Turkiya ta bayar da umarnin cafke mutane biyu 'yan kasar Saudiyya wadanda suke da hannu kai tsaye wajen aiwatar da kisan Jamal Khashoggi.

Tashar Rusia Yaum ta bayar da rahoton cewa, Kotun kolin da ke da mazauninta a birnin Istanbul ta sanar da cewa, Qahtani da Asiri su ne suke da hannu kai tsaye wajen shirya dukkanin hanyoyin da aka bi wajen kisan Khashoggi.

Kotun ta ce ta bayar da umarni d a kame mata wadannan mutane guda biyu domin gurfanar da su a gabanta kan wannan mummunan laifi da suka aikata.

Ahmad Asiri shi ne shugaban hukumar leken asiri ta kasar Saudiyya, yayin da Qahtani shi ne babban mai bayar da shawara kan harkokin tsaro ga masarautar Saudiyya, kuma na hannun damar Muhammad Bin Salman.

Kotun ta ce mika wadannan mutanen biyu zai taimaka ma Saudiyya ta samu sauki matsin lambar da take fuskanta daga kasashen duniya.

3769887

 

 

Wanda Aka Watsa: 1
Ana Cikin Dubawa: 0
Ba A Iya Watsa Shi: 0
Ba A San Shi Ba
0
0
Allah ya la'anci sarakunan saudia ko dabba akayiwa kisan da akayiwa Jamal wallahi Allah bazai bariba dama irin wannan kisan aikinsune .
captcha