IQNA

An Bude Gasar Kur’ani Ta Duniya A Tunisia

19:42 - December 09, 2018
Lambar Labari: 3483199
Bangaren kasa da kasa, an bude babbar gasar kur’ani ta duniya a jami’ar Malik Bin Anas a birnin Qartaj na kasar Tunisia.

Kamfanin dillancin labaran iqna, shafin yada labarai na DMCA ya bayar da rahoton cewa, a jiya Asabar ne aka bude taron babbar gasar kur’ani ta duniya karo na 16 a jami’ar Malik Bin Anas a birnin Qartaj na kasar Tunisia , mai taken Allah bin Arafah, wadda ministan harkokin adini na kasa Ahamd Azum ya jagoranci budewa.

Ahamd Al-sawafi daga Oman da Amir Amushri daga Aljeriya, da Aus Al-Utaibi daga Jorda, sai kuma Hamd Al-hashash daga Bahrain, su ne suka fara gudana da karu a ranar farko ta gasar.

A bayanin da ya gabatar a wajen bude gasar, Aham Naufal daga ma’aikatar kula da harkokin addinia  Tunisia ya bayyana cewa, a wannan karon an kara bangaren tafsirin kur’ani a cikin bangarorin gasar.

Kasashe da dama ne suke halartar gasar, da suka hada da Aljeriya, Iran, Saudiyyah, Mauritaniya, Libya, Masar, Jordan, Oman, Qatar, Palastine, Russia, Sudan, Kuwait, UAE, Bahrain, Malaysia, Indonesia, Iraki, Lebanon da sauransu.

3770668

 

 

 

captcha