IQNA

Wata Cibiyar Kididdiga Ta Zabi Gwaran Shekara Ta 2018

23:59 - January 01, 2019
Lambar Labari: 3483274
Cibiyar Nazari da kididdiga kan lamurran siyasar kasa da kasa a Joradn ta zabi Ahad Tamimi da Mahatir Muhammad a matsayin gwaran sheakra ta 2018 da ta gabata.

Kamfanin dillancin labaran iqna, babbar cibiyar da ke yiin nazari tare da fitar da alkalumma kan wasu batutuwa da suka shafi siyasar kasa da kasa a Joradn , ta bayyana cewa ta zabi Ahed Tamimi bafalastinya 'yar shekaru 17 da haihuwa a matsayin babbar jaruma ta shekarar 2018, sakamakon yadda ta yi tsayin daka a gaban sojojin Isra'ila, wanda hakan yasa har aka tsare ta a gidan kaso na wani lokaci.

Bayan fitowar Ahed Tamimi daga gidan kason Isra'ila, ta ci gaba da gwagwarmaya ta neman kare hakkokin Falastinawa da suke cikin mawuyacin hali na tsangwama da cin zarafi a karkashin gwamnatin yahudawan Isra'ila, inda cibiyar ta ce wannan matsayi na Ahed ya cancanci yabo da kuma bayyanata jarumar shekara.

Sai kuma Mahatir Muhammud wanda tsohon firayi ministan kasar Malayisia ne wanda ya sake dawowa kan mukaminsa yana da shekaru 93 a duniya, kamar yadda kuma yake daya daga cikin shugabanni masu nuna adawa da duk wani nau'in zalunci kan al'ummar Palastine, wanda hakan babbar jarunta ce da wani shugaba daya cikin shugabbanin kasashen duniya ya nuna da ta cancanci yabo.

3777693

 

 

 

 

captcha