IQNA

Bayani Kan Hakkokin Mata A Baje Kolin Littafai Na Alkahira

16:05 - January 27, 2019
Lambar Labari: 3483332
Bangaren kasa da kasa, an gudanar da lacca laccoci kan abin da ya shafi hakkokin mata a gefen taron baje kolin littafai na kasa da kasa a birnin Alkahira.

Kamfanin dillancin labaran iqna, shafin yada labarai na masrawy cewa, an gudanar da lacca laccoci kan abin da ya shafi hakkokin mata a gefen taron baje kolin littafai na kasa da kasa a birnin Alkahira wanda Abdulmun’im Fu’ad shugaban bangaren bincike kan harkokin ilimin musluci na jami’ar Azhar da Nahla Saidi suka gabatar da jawabai.

Abdulmun’im Fu’ad ya bayyana cewa, mata suna da matsayi a cikin addinin muslunci, wanda yake tabbatar da cewa muslunci shi ne jag aba wajen kare hakkokin mata da ma ‘yan adam baki daya.

Ya ci gaba da cewa babbar manufar ware lokaci domin gabatar da jawabi kan matsayin mata a addinin musluni shi ne, fito da abubuwa da aka jahilta dangane da mata da kuma matsayinsu a cikin addinin muslunci, domin muslunci na kallonsu a matsayin makaranta ta farko ta tarbiyar dan adam.

Nahla Saidi, a lokacin da take gabatar da nata jawabin ta jaddada cewa, irin matsayin da musulunci ya baiwa mata matsayi ne na karamci da girmama matsayinsu, da kuma kare dukkanin hakkokinsu a cikin rayuwar zamantakewa.

3784688

 

 

 

 

 

captcha