IQNA

Taron Karawa Juna Sani A Istanbul Kan Makomar Musulmi A Turai

22:28 - March 08, 2019
Lambar Labari: 3483436
Bangaren kasa da kasa Taron ya gudana ne a birnin Istanbul na kasar Turkiya tare da halartar masana daga kasashen duniya daban-daban.

Kamfanin dillancin labaran iqna, Kamfanin dillancin labaran Anatoli ya bayar da rahoton cewa, a yayin gudanar da zaman taron Farfesa Rajab Shan Turk shugaban jami’ar Ibn Khaldun ta kasar Turkiya ya bayyana cewa, wannan zaman taro shi ne irinsa na farko da aka fara gudanarwa.

Babbar manufar taron dai ita ce yin dubi kan halin da musulmi suke ciki a nahiyar turai, da kuma duba bangarorin da suke fuskantar matsaloli domin daukar matakai na magance su, kamar yadda kuma taron yake da nufin bude wata kofa ta tattaunawa tsakanin masana musulmi da kuma masana na nahiyar turai kan batutuwa daban-daban da suka shafi alaka a tsakaninsu.

Shi ma a nasa bangaren Farfesa Polent Aucher masani kan harkokin zamantakewa daga kasar Jamus fadi a yayin da yake gabatar da jawabi a wurin taron cewa, akwai bukatar kara fadada nazari a nahiyar turai kan addinin muslucni, domin da dama daga cikin al’ummar turai hard a wasu masana a nahiyar, suna da karancin masaniya kan addinin muslucni.

Ya kara da cewa hakika musulmi suna fuskantar matsaloli masu tarin yawa a turai, amma ta hanyar wayar da kai da shirya taruka da fitar makaloli za a samu ci gaba, da kuma samun kyakkayawar dangantaka.

3796129

 

captcha