Kamfanin dilancin labaran iqna, Amru Saad ya bayyana cewa, a lokacin da ya bayar da wani fim dinsa kyauta ga Mike Tyson wanda ya kunshi wasu ayoyin kur’ani tsarki, a lokacin Tyson ya ji abin da ayoyin suka kunsa a nan take ya zubar da hawaye.
Wannan dan wasa na kasar Masar ya ce Mike Tyson mutumin kirki ne, domin kuwa na kasance tare da shi a lokacin da ya ziyarci Masar, mun je wasu wurare tare shi, saboda haka na ga halayensa.
An haifi Tyson ne a shekara ta 1966 a yankin Broklyn na birnin New a kasar Amurka, kuma ya tashia yankin, inda a shekara ta 1992 aka daure shi tsawon shekaru biyu a gidan kaso, bayan fitowarsa kuma ya tasirantu matuka da addinin mulsunci.
Kafin nan yay i tafiya zuwa Saudiyya inda ya y aikin Umrah, ya kuma ziyarci wasu wurare masu tsarki da suke a cikin kasar.
Dangane da tafiyarsa zuwa Umra Mike Tyson ya bayyana cewa hakika ya yi farin ciki maras misiltuwa, tun ya ziyarci wurare masu tsarki na addinin muslunci.