IQNA

Musulunci Na Samun Karbuwa Cikin Sauri A Rwanda

22:32 - April 06, 2019
Lambar Labari: 3483525

Kamfanin dillancin labaran iqna, Tashar talabijin ta TR World ta bayar da rahoton cewa, sakanmakon wani bincike da aka gudanar a kasar Rwanda ya nuna cewa, tun bayan yakin basasar da aka yi fama da shia kasar kimanin shekaru 25 da suka a cikin shejkarun 1994, ya zuwa yanzu addinin muslunci ya samu karbuwa a kasar fiye da sauran addinai da ba na kiristanci ba.

Matabaro Sulaiman wanda tsohon malamin addinin kirista ne, ya bayyaa cewa; a lokacin yakin basasa sun ga an mayar da wasu majami'oin mabiya addinin kirista sun zama wurin kashe 'yan adam saboda banbancin kabila, sabanin musulmi wadanda suke bude kofofin masallatai suna karbar mutane suna taimaka musu, suna ba su abinci, da kuma yi wadanda suka samu raunuka magani.

Ya ce wannan lamari ya yi gagarumin tasiri a cikin zukatan jama'a, inda suka yi ta karbar addinin muslunci, kuma har yanzu hakan an ci gaba, wanda a cewarsa, wanann ne ya yi sanadin har ya karbi muslucni.

Shi ma a nasa bangaren tsohon babban mufti na kasar Rwanda Salim habimana ya bayyana cewa, daga shekarar 1884 lokacin da turawa suka fara yi wa kasar mulkin mallaka har zuwa lokacin samun 'yancin kai, al'ummar kasar suna bin addinin kirista a karkashin darikar Katolika ne, inda adadin muslumi bai wuce kashi daya cikin dari ba, amma daga bayan yakin basasar kasar ya zuwa yanzu, adadin muslunci kasar Rwanda ya kai kashi goma sha biyar an al'ummar kasar.

3801119

 

 

captcha