IQNA

23:04 - April 08, 2019
Lambar Labari: 3483533
Kungiyoyin addini  da farar hula a kasar Malaysia, sun bukaci da aka kai dauki ga al’ummomin kasar Iran da ambaliyar ruwa ta shafa.

kamfanin dilalncin labaran iqna, A cikin wani bayani da ya karanta a gaban manema labarai a madadin kungiyoyin addinin muslucni da kuma giyoyin farar hula na kasar Malaysia, shugaban majalisar kungiyoyin addini na kasar Mahad Azmi Abdulhamid ya bayyana cewa, suna yin kira ga dukaknin al’ummomin duniya da su kai dauki ga al’ummomin da ambaliyar ruwa ta shafa a kasar Iran.

Ya ce takunkuman da Amurka ta kakaba wa Iran ba dalili ne da zai hana kasashen muslmi da kungiyoyin agaji na kasa da kasa musamman na majalisar dinkin duniya, kai taimako ga al’ummar Iran da ambaliyar ruwa ta shafa ba, fakewa da hakan kuma wajen kin taimaka Iran ya sabawa kaida da tsarin da aka kafa majalisar dinkin duniya a kansa.

Shi ma a nasa bangaren babban malami mai bayar da fatawa a kasashen yankin gabashin nahiyar Asia Sheikh Abdulganiyi Shamsuddin ya bayyana cewa, a duk lokacin da wani bala’i ya samu wata kasa a duniya muna ganin yadda kasashen duniya da kungiyoyi suke kai taimako, amma me yasa da ambaliyar ruwa ta shafi wasu yankunan Iran sai duniya ta yi shiru?

Ya ce ina kungiyar OIC mene ne ta yi na taimaka ma musulmin Iran? Ya ce abin da yake faruwa a zahiri ya kama da munafunci na siyasa, alhali wannan batu ne na ‘yan adamtaka da bai kamata a saka batun siyasa a cikinsa ba.

3801902

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، Iran ، malasia ، ambaliyar ruwa
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: