IQNA

20:18 - April 09, 2019
Lambar Labari: 3483535
Sojojin kasar Amurka uku sun hakala a kasar Afghanistan, biyo bayan wani harin bama-bamai da aka kai kansu a sansanin soji na Bagram.

Kamfanin dillancin labaran iqna, ya bayar da rahoton cewa, a yammacin jiya Litinin an kai wa sojojin Amurka da ke aiki a cikin rundunar NATO hari a kasar Afghanistan, tare da hakala uku daga cikinsu, da kuma jikkata wasu uku na daban.

Rahoton ya kara da cewa baya ga sojojin Amurka uku, harin ya yi sanadiyyar mutuwar wani mutum da yake aiki tare da sojojin na Amurka, wanda ba a bayyana kasarsa ba.

Tuni dai kungiyar Taliban a ta bakin kakakin kungiyar Zabihullah Mujahid, ta sanar da cewa ita ce take da alhakin kai harin.

Zabihullah Mujahid ya bayyana cewa, sun kai harin ne a kan wato sojojin mamaya, kuma sun samu nasarar halaka wasu daga cikinsu.

Sojojin Amurka sun kafa shingaye a wurin da lamarin ya faru, tare da daukar tsauraran matakan tsaro.

3802081

 

 

 

 

 

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: