IQNA

22:57 - April 15, 2019
Lambar Labari: 3483549
Bangaren kasa da kasa, wani mabiyin addinin kirista  akasar masar ya bayar da wani babban fili domin gina cibiyar hardar kur’ani mafi girma a lardin Buhaira.

Kamfanin dillancin labaran iqna, shafin yada labarai na Alfarja ya bayar da rahoton cewa, wani mabiyin addinin kirista a lardin Buhaira da ya  nemi a boye sunansa, ya bayar da wani babban fili domin gina cibiyar hardar kur’ani mai tsarki mafi girma  alardin baki daya.

Daya daga cikin manyan daraktocin ma’aikatar kula harkokin addini ta kasar Masar Jabir Tai ya bayyana cewa, wannan babban lamari da ya kamata ya zama darasi ga dukkanin al’ummar kasar Masar, da ma dukkanin mutane a duniya.

Ya ce hakika al’ummar Masar sun kasance suna rayuwa tare da juna musulmi da kirista, kuma suna rayuwa a matsayin ‘yan uwan juna, baya ga haka kuma akwai taimakekeniya a tsakaninsu, amma wannan abin day a faru na musamman ne, wanda ko shakka babu zai yi gagarumin tasiri wajen kara dankon kauna tsakanin mabiya addinan kirista da musulunci a kasar.

Kafin zuwan addinin musluci dai kiristanci ne addinin kasa a Masar, kuma kabilar Kibdawa wadda ita ce ke bin addinin kirista a halin yanzu a kasar Masar, ta kasance daddiyar kabila a kasar, wadda tarihi ba zai taba mantawa da ita ba.

3803857

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: