IQNA

An Cafke Wani Mutum Da Ya Sake Yin Barazar Kisan ‘Yan Majalisa Musulmi A Amurka

23:52 - April 21, 2019
Lambar Labari: 3483565
Bangaren kasa da kasa, jami’an tsaron kasa Amurka sun cafke wani mutum da ya yi barazanar kashe ‘yan majalisar dokokin Amurka musulmi.

Kamfanin dillancin labaran iqna, tashar talabijin ta Aljazeera ta bayar da rahoton cewa, jami’an tsaron kasa Amurka sun cafke John Claisse wani mutum daga jahar Florida da ya yi barazanar kashe ‘yan majalisar dokokin Amurka musulmi, wato Rashida Tlaib da kuma Ilhan Omar.

John Claisse ya yi da’awar cewa Ilhan Omar ba dauki batun harin 11 ga watan Satumban 201 da muhimmanci ba.

Ihan Omar da sauran ‘yan majalisar dokokin Amurka daga jam’iyyar Democrat sun mayar da martani kan batun, tare da bayyana kalaman nasa da cewa na nuna kyama ne kawai.

Kafin wannan lokacin dai Claisse ya gargadi duk wasu ‘yan siyasa da suke sukar Donald Trump da cewa su shiga taitayinsu.

A cikin watan Maris din ya gabata ma wata kotu a birnin New York ta yanke hukuncin daurin shekaru 12 kan wani mutum da ya yi barazanar kashe Ilhan Omar.

3805182

 

 

 

 

captcha