IQNA

23:53 - May 02, 2019
Lambar Labari: 3483598
Qatar ta nuna rashin amincewa da takunkuman da Amurka ta kakaba wa kasar Iran.

Kamfanin dillancin labaran iqna, ya bayar da rahoton cewa, a lokacin da yake amsa tambayoyin manema labarai a jiya birnin Doha fadar mulkin kasar Qatar, ministan harkokin wajen kasar Qatar Muhammad Bin Abdulrahman Al Thani ya bayyana cewa, takunkuman da Amurka ta kakaba wa Iran suna da mummunan tasiri ga kasashe masu danyen man  fetur.

Ya ce matakin da Amurka ta dauka bai dace ba, domin kuwa ko shakka babu wannan takunkumi ba kasar Iran kawai zai cutar ba kamar yadda Amurka take tsammani, hakan zai cutar da dukaknin kasashen masu  sayen danyen mai daga Iran, da kuma masu sayen mai a kasuwanninsa na duniya.

Ministan na Qatar ya ce kasarsa ba za ta yi aiki da takunkumin na kasar Amurka a kan kasar Iran ba.

3808134

 

 

 

 

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، kasarsa ، Qatar ، Iran
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: